TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 3

TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 3 Post Featured Image || ahmadabdulnasir.com.ng

ASALIN TUNANI - TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA. WA KE SAMAR DA TUNANI? PART THREE


Binciken Malaman Kimiyya na Farko kan Kwakwalwa

A makon da ya gabata masu karatu sun karanta bayanai kan hakikanin yadda halittar zuciya da kwakwalwa suke a kimiyyance, da kuma irin yadda bincike ya faro kan wadannan gabobin jikin dan adam masu muhimmanci tun daruruwan shekaru da suka gabata. Kada a mance dai, muna gudanar da bincike ne dalla-dalla kan asalin tunani tsakanin zuciya da kwakwalwar dan adam; wanne ne yake da hakkin samar da tunani? A yau cikin yardar Allah ga bayanai kan binciken malaman kimiyyar halitta na farko kan wasu daga cikin yanayin da suka shafi zuciya dangane da alakarta da kwakwalwa, da kuskure ko daidai din da binciken ya kunsa. Wannan shi ne bincike na uku. A mako na gaba za mu kawo tsarin tunani a kwakwalwa kamar yadda malaman kimiyyar halittar dan adam ke karantarwa a jami'o'in duniya a yau. Sannan mu karkare da bincike kan sabon nau'in binciken da ya bullo kan alakar kwakwalwa da zuciyar dan adam, inda a karshe za mu tantance gabar da ke samar da tunani a tsakaninsu; zuciya ce ko kwakwalwa. Allah sa mu dace.

Bayan sun gudanar da bincike kan hakikanin yadda zuciya da kwakwalwa suke aiki, malaman kimiyyar halittar dan adam a baya sun fitar da sakamakon wasu bincike wadanda a farko aka dogara kansu wajen fahimtar tsarin gudanarwar kwakwalwa da alakarta da zuciya. Binciken farko kan alakarta da bugun zuciya ne. Bincike na biyu kuma kan alakar kwakwalwa ne da babbar tsarin sadarwar jiki baki daya, watau Automatic Nervous System. Sai bincike na uku da ya shafi tsarin sadarwa tsakanin zuciya da kwakwalwa. A halin yanzu ga bayani nan filla-filla.

Bincike na Farko

Nau'in sakamakon bincike na farko da malaman kimiyya suka gudanar a baya ya ta'allaka ne kan kwakwalwa da bugun zuciya. Suka ce kwakwalwa te ke haddasa bugun zuciya (watau Heartbeat), ta amfani da jijiyoyin tsarin sadarwar jiki, watau Automatic Nervous System (ANS). Wannan na daga cikin dadaddun bincike da malaman kimiyyar halittar dan adam suka yi kan wannan lamari. Amma daga baya, bayan habbakan hanyoyin bincike da karuwar ilmi, an gano cewa babu alaka tsakanin bungun zuciya da taimakon kwakwalwa ko kadan, ta wannan bangare. An kuma gano kuskuren wannan bincike ne lokacin da aka fara aiwatar da tiyata ko dashen zuciya. A halin yanzu an tabbatar da cewa zuciya ba ta bukatar wayoyin sadarwar da za su samar mata da makamashin maganidisun lantarki don haddasa bugawarta. Domin ita kanta tana dauke da irin wadannan wayoyin jijiyoyin sadarwa wajen sama da dubu arba'in (40,000), wadanda ke rike ta, tare da taimaka mata wajen bugawa a kowane lokaci. Don haka ba ta bukatar taimakon wadannan wayoyin sadarwa daga kwakwalwa. A karshe, gaskiyar sakamakon wannan bincike yana fitowa fili karara a duk lokacin da ake aikin dashen zuciya. Idan aka zo cire matacciyar zuciyar, ana yanke dukkan jijiyoyin wayoyin sadarwar da suka zo daga kwakwalwa ne, sannan sai a jona sabuwar da ake son dasawa. An gano cewa da zarar an dasa sabuwar, kafin a jona wayoyin jijiyoyin sadarwar da suka zo daga kwakwalwa, nan take zuciyar ke fara aiki. Don haka, da bugun zuciya na samuwa ne ta taimakon wayoyin jijiyoyin sadarwar da suka zo daga kwakwalwa, da babu yadda za a yi wannan sabuwar zuciya da aka dasa ta kama aiki ba tare da an jona mata jijiyoyin da suka taso daga kwakwalwa ba. Nan take aka sake gudanar da bincike cikin zuciya don gano dalilin hakan, sai aka samu akwai ire-iren wadancan wayoyin sadarwa (watau Nerve Cells) a zuciya sama da dubu arba'in.

Bincike na Biyu

Sakamakon bincike na biyu an fitar da shi ne a shekarar 1970, kamar yadda Cibiyar Binciken Kimiyya da ke Fels ta kasar Amurka ta tabbatar, watau Fels Research Institute, kuma abin da sakamakon ya tabbatar a wancan lokacin dai shi ne: gamammen tsarin sadarwar jikin dan adam (Automatic Nervous System) ne ke hada alaka tsakanin zuciya da kwakwalwar dan adam. Sakamakon wannan bincike, kamar wanda ya gabace shi, bai dore ba. Domin bayan tsawon zamani da samuwar karin hanyoyin bincike, an gano cewa ba wannan tsarin sadarwa bane ke hada alaka tsakanin zuciyar dan adam da kwakwalwarsa. Bayanai na tafe kan bangarorin jikin da ke haddasa wannan tsarin sadarwa, in Allah ya so.

Bincike na Uku

Bincike na uku an gudanar da shi ne a shekarar 1983, kuma abin da sakamakon binciken ke cewa shi ne: akwai wasu sinadaran sadarwar jiki da a Turancin kimiyya ake kira Hormones, masu dauke da maganadisun lantarkin sadarwa, su ne ke haddasa alakar sadarwa a tsakanin kwakwalwa da zuciyar dan adam. Wannan sabon bincike ne ya inganta, ko ya gyatta kuskurarriyar fahimtar da ake da ita kan binciken shekarar 1970 da ya gabata, cewa gamammen tsarin sadarwar jiki ne ke hada alaka tsakanin zuciya da kwakwalwa. Wannan sabon bincike dai ya dada samun shahara ne daidai lokacin da cibiyar bincike ta HeartMath Institute da ke jihar Kalfoniya ta gudanar da bincike kan hakikanin gabar jikin dan adam da ke samar da tunani.

Binciken cibiyar HeartMath ya tabbatar da cewa wadannan sinadarai masu gamewa a jikin dan adam, su ne ke daukan maganadisun lantarkin sadarwa – watau Electromagnetic waves – daga zuciya, zuwa dukkan sassan jikin dan adam, ciki har da kwakwalwa. Shi yasa da zarar zuciyar dan adam ta hankalci canji a yanayin da take, (misali a ce ka shigo inda ake ta hayaniya, ko zage-zage tsakanin mafadata biyu, nan take zuciyarka za ta hankalci yanayin da ta shiga, sai ta aika wa sauran gabobin jiki, sai dabi'arsu ta canza). Wannan tsarin aika sako na samuwa ne cikin kiftawa da bisimilla, ta hanyar wadannan sinadaran Hormones da ke kaikomo tsakanin zuciya da sauran gabobin jiki, ciki har da kwakwalwa. Wadannan, a takaice, su ne nau'ukan bincike uku da aka fara gudanarwa a baya wadanda suka danganci alakar da ke tsakanin kwakwalwa da zuciyar dan adam wajen aikawa da sako, wanda hakan, ko shakka babu, yana da alaka ta kai-tsaye wajen kintsa tunani.


Tsakanin Nassin Kur'ani da Binciken Malaman Kimiyya

To, a daya bangaren kuma wasu kan damu cewa, me yasa idan masu bincike suka ce abu kaza kaza ne, daga baya kuma sai su sake cewa ba haka bane, kaza ne. Wannan yasa da yawa cikin mutane, musamman a kasar Hausa, basu cika yarda da binciken Malaman Kimiyyar zamani ba kan wasu abubuwa da suka shafi halittar dan adam, ko sararin samaniya da dai sauran abubuwa makamantansu. A wasu lokuta za ka samu abin da Malaman Kimiyya suka fada a baya ya saba wa abin da Kur'ani ya tabbatar, daga baya kuma idan suka zurfafa bincike, sai sakamakon bincikensu ya tabbatar da abin da Kur'ani ya fada. Al'amura irin wannan sun sha faruwa a baya. Daga cikin shahararrun misalai akwai binciken malaman kimiyya a farkon zamani cewa Rana ba ta motsawa, sai dai sauran halittun sararin samaniya. Amma Kur'ani ya tabbatar da cewa rana tana juyawa ita ma a cikin falakinta, kamar yadda hakan yake tabbace a cikin Suratu Yaasin. Da bincike ya tsawaita, sai malaman sararin samaniya suka tabbatar cewa lallai Rana ita ma tana juyawa, ba Wata da sauran Taurari kadai ke juyawa ba. Me yasa ake samun haka? Shin, wannan sabani da a farko ake samu tsakanin nassin Kur'ani ko Hadisi da sakamakon binciken malaman kimiyya, dalili ne da zai sa a daina yarda da bincikensu baki daya?

A tunani na hakan ba dalili bane, ko kadan. Illa dai, a matsayinmu na musulmi, duk abin da Kur'ani ya tabbatar da shi wajibi ne mu gasgata shi, ko da kuwa ba mu iya hankaltar faruwa ko yiwuwarsa a lokacin da aka gaya mana. Domin nassin Kur'ani ko Hadisi ba su canzawa, amma binciken duk wani mai bincike, yana iya dacewa, sannan yana iya kuskure. Abin da ke nuna dacewarsa shi ne yayi daidai da abin da nassin shari'a ya tabbatar. Abin da zai nuna kuskurensa kuma shi ne ya saba wa abin da nassin shari'a ya tabbatar. Domin masu gudanar da binciken nan 'yan adam ne kamarmu. Bambancin da ke tsakaninmu (wadanda ba masana ko kwararru a fannin) da su, shi ne, suna da kwarewa da kuma mizanin ilmi da suke amfani da su; ba wai da ka kawai suke kiyastawa su ce abu kaza kaza bane. Don haka wajibi ne a kan kowane Musulmi muddin Kur'ani ya tabbatar da samuwa ko yiwuwa ko yanayin wani abu, to, dole ne ya gasgata shi, ko da kuwa ba ya iya fahimta ko hankaltar abin a zahiri ko a hankalce; kuma ko da binciken mai bincike ya tabbatar da akasin abin da Kur'ani ya tabbatar.

Amma muddin Kur'ani bai fada ba, ko kuma bai tantance wani abu ba, idan masu bincike suka ce ga yanayinsa, ko ga yadda yake faruwa, ko kuma abu kaza kaza ne, to a nan ba wajibi bane sai ya gasgata bincikensu. Idan kuma malaman kimiyya suka tabbatar da wani abin da Kur'ani bai tabbatar ba, musamman kan tarihin baya, to a nan shi ma sai dai ka yi zugum; kada ka gasgata, kuma kada ka karyata. Misali, dukkan malaman musulunci sun yarda cewa babu wanda ya san adadin shekarun wannan duniyar da muke rayuwa a cikinta sai Allah. Dukkan hadisan da suka zo masu nuna adadin shekarun duniya ko na rana ko na wata, duk masu rauni ne, ba a kafa hujja da su. Don haka idan malaman kimiyya suka ce duniya ta yi shekaru kaza ne, to a nan sai dai kayi shiru kai Musulmi; kada ka karyata, kuma kada ka gasgata. Domin zai iya yiwuwa abin da suka fada haka ne, zai iya yiwuwa kuma ba haka bane; tunda ba da ka suka fada ba, kuma ba sihiri suka yi wajen gano hakan ba, sun bi dalilai ne na alamun da suka bayyana musu. Idan kayi shiru a nan ka fitar da kanka daga tuhuma, tunda daman Allah bai wajabta maka yin imani ko rashin imani da hakan ba.

Abin da yasa na kawo wannan bayani shi ne, nan gaba za mu ci karo da abubuwa makamantan wanNan, ba sai na maimaita mana dalilin faruwansu ba. Allah sa mu dace, ya kuma amfanar da mu abin da ya sawwake mana nemansa na ilmi, amin.

About Author  
 Picture
Ahmad Abdulnasir Shuaib
TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 2 Blog Post Header Image TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 3 Header Image TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 4 Blog Post Header Image TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 3 Header Image