TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 2

TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 2 Post Featured Image || ahmadabdulnasir.com.ng

ASALIN TUNANI - TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA. WA KE SAMAR DA TUNANI? PART TWO


Tsarin Halittar Zuciya da Kwakwalwar Dan Adam

Jikin dan Adam na dauke ne da bangarori nau'uka daban-daban, masu kamanni daban-daban, a wurare daban-daban, don aiwatar da ayyuka daban-daban, a yanayi daban-daban, cikin umarni mai dauke da girman kudurar Ubangiji mahaliccin bayinsa masu kamanni da kintsi daban-daban. Halittar dan adam abu ne mai matukar ban al'ajabi, cike da hikima da kwarewar da babu wanda zai iya samar da ita har abada. Daga cikin muhimman bangarorin jikin dan adam da yake ji da su saboda kebantacciyar matsayinsu wajen tafiyar da rayuwarsa, akwai zuciya da kuma kwakwalwa. Wadannan bangarorin jiki na dan adam sun shahara sosai, saboda kebantattun aikin da suke gudanarwa a jikinsa. Ba ma shi kadai ba, malaman kimiyya sun tabbatar, ta hanyar bincike na kwakwaf, cewa dukkan dabbar da ke da kashin baya (watau Backbone, ko Vertebral Column, ko Spinal Column), to, tana dauke da kwakwalwa da kuma zuciya. Kamar yadda bayanai suka gabata a makon jiya, yau ga mu dauke da bayani kan halittar zuciya da kwakwalwar dan adam. Wadannan bayanai sun ta'allaka ne kai tsaye ga sifofinsu, da ayyukansu, da kuma yanayinsu a jikin dan adam; a mahangar malaman kimiyyar halitta na zamani.

Zuciyar Dan Adam

Zuciyar dan adam wani curin nau'in nama ne mai gautsi, mai asali daga yadin jijiyoyin jikinsa masu taushi da a harshen Turanci ake kira Cardiac Muscle. Wannan curin nama na dauke ne cikin kogon kirjin dan adam, daga bangaren hagunsa. Girman zuciya duk bai shige dunkulen yatsun dan adam matashi ba. Kuma tana dauke ne da wasu kwaroron jijiyoyi guda hudu masu taimakawa wajen shigi-da-ficin jini a bangaren dama da hagu, da bangaren sama da kasanta. Akwai bambanci tsakanin girma da nauyin zuciyar namiji da zuciyar mace. A yayin da nauyin zuciyar namiji ke tsakanin giram 300 – 350, nauyin zuciyar mace bai wuce tsakanin giram 250 - 300 ba. Allah kadai ya san hakikanin hikimar da ke tsakanin bambanta girmansu.

Zuciyar dan adam na gudanar da ayyuka masu dimbin yawa wadanda har yanzu malaman kimiyyar halittar jikin dan adam sun kasa tantance adadinsu. Abin da ake ta yi dai shi ne bincike, har zuwa wannan lokaci da nake wannan rubutu. Amma muhimmi daga cikin ayyukan zuciya da ake iya gani da jinsa, shi ne lura da babban tsarin sadar da jini ga dukkan bangarorin jikin adan adam; daga yatsun kafafunsa zuwa jijiyoyin kwakwalwarsa, dare da rana da safe da yamma. Zuciya ce ke taimaka wa tsarin gewayen jini a jikin dan adam (watau Circulatory System), wajen fanfon jini daga kasa zuwa sama, da akasin hakan. Zuciya ce injin da ke fanfon jini a wannan tsari. Wannan aiki na samuwa ne ta hanyar bugun zuciya (Heartbeat) da ke samuwa a duk sadda zuciyar ta takura (don harba jini) sannan ta sake (don jawo jini) daga wani bangare zuwa wani bangare. An kiyasta cewa zuciyar kowane matashi kan buga sau 72 a cikin minti daya.

Malaman kimiyyar halittan jikin dan adam sun tabbatar da cewa zuciyar dan adam na fara aikinta ne (ta hanyar bugawa don aikawa da karban jini a jiki), makonni uku da gama tsara halittar dan tayi a mahaifa. Ma'ana, da zarar Allah ya busa rai a jikin dan tayin da ke mahaifa, nan take zuciyarsa ke fara aikinta. Kuma haka za ta ci gaba da bugawa har tsawon rayuwarsa. Wadannan jijiyoyi da ke aikin takurawa da sakewa a zuciya ba su samun hutu sai na 'yar tazarar lokacin da ke tsakanin takura da sakewar. Ma'ana, tsawon lokacin da bai kai dakika daya ba kenan. Bincike ya kuma tabbatar da cewa, mutumin da zai yi shekaru 76 a duniya, zuciyarsa za ta buga sau biliyan biyu da miliyan dari takwas (2.8 billion beats), kuma za ta harba jinin da adadinsa ya kai lita miliyan 169 a yayin wannan bugawa nata. Dankari! Wannan ke nuna cewa a dukkan jikin dan adam, babu bangaren da yafi zuciyarsa tsawon lokacin aiki, da yawan aiki, da kuma inganci wajen halitta. Duk da cewa sauran suna da inganci su ma.

Masana basu gushe ba tun farkon zamani wajen binciken halin da zuciyar dan adam ke aiki a yanayi daban-daban. Daga lokacin da aka fara rubutun tarihi zuwa yanzu, an gano abubuwa da dama dangane da abin da ya shafi zuciyar dan adam. Wadanda tarihi ya tabbatar da kokarinsu dai su ne likitocin Kibdawan kasar Masar, sai kuma likitocin Girkawa (Greek Physicians), sai likitocin Daular Rumawa. Daga nan sai likitocin karni na 16 da 17 da suka tagaza nasu kokarin, wajen binciko bangaren jikin dan adam da ke da alhakin harba jini zuwa sauran bangarorin jikinsa. Kokarin masana irin su Michael Servetus da William Harvey ne ya taimaka wajen gano hakikanin bangaren da ke wannan aiki; watau zuciya. Muna shiga karni na 20 kuma sai wannan tsarin bincike ya dauki wani sabon salo, inda aka samu likitan farko da yayi kurum wajen gunadar da tiyar zuciya (Heart Surgery) na farko a duniya a kasar Amurka. Wannan likita kuwa shi ne L.L. Hill, a shekarar 1902. A wannan karni ne har wa yau aka gudanar da bincike don samar da na'urar binciken zuciya, watau ECG. Wanda yayi wannan hobbasa kuwa shi ne wani likita dan kasar Jamus mai suna Willem Einthoven, a shekarar 1924. Daga nan dai tsarin bincike ya ci gaba da habaka, har muka samu kanmu cikin wannan zamani mai dauke da nau'urori kala-kala da ake amfani da su wajen gwajin bugun zuciya, da na daukan hoton zuciya, da wukaken da ake amfani da su wajen yin tiyatar zuciya da dai sauran makamantansu. A farkon lamari likitoci basu yarda cewa za a iya yi wa zuciya tiyata ba, saboda tsananin taushi da gautsin da ke tattare da ita. Har sai da likita L.L. Hill ya gwada yi wa wani yaro dan shekaru 8 a shekarar 1902, kamar yadda bayani ya gabata. Don haka, a mahangar malaman kimiyyar halittar dan adam (Physiologists), muhimmin aikin zuciya shi ne samar da bugawar jini zuwa sassan jiki, da kuma daidaita harbawar zuciya, da taimaka wa sauran bangarorin jiki wajen samar da jini mai dauke da sinadaran iska, don tafiyar da rayuwa.

Kwakwalwar Dan Adam

Kwakwalwar dan adam wani curin gungun jijiyoyin yadi ne masu dauke da sinadaran kara kuzari (Protein), da hanyoyin jini, wadanda kuma ke kunshe cikin kokon kan dan adam (Human Skull). Wannan curin gungun jijiyoyi na da sila ne na kai tsaye da kashin bayan jikin dan adam, kuma wani bangare ne mai muhimmanci wajen hada alaka tsakanin dukkan bangarorin jiki, ta hanyar babbar tafarkin sadarwar bayanai na jikin dan adam, watau Central Nervous System kenan. Kwakwalwar dan adam ce ke lura da kuma tafiyar da tsarin rayuwarsa ta hanyar bayanai da sadar da su. Ita kwakwalwa kamar yadda malaman kimiyyar halitta suka tabbatar a binciken baya, wata cibiya ce da ke da tasiri wajen aiwatar da sadarwa ga dukkan bangarorin jikin dan adam. Ita ce bangaren da ke lura da dabi'ar kauna, da tsana, da tsoro, da fushi, da farin ciki, da bakin ciki. Har wa yau malaman kimiyyar halitta sun danganta kwakwalwa da samar da tunani, da hazaka, da koyon harshe, da tantance abubuwa, da haddace bayanai, da kuma tuno su bayan haddace su. Ita ce ke lura da bacci, da kishirwa, da dabi'un da ke lura da rayuwar dan adam baki daya.

Yadda kwakwalwa ke aiki abu ne mai matukar ban al'ajabi. Wannan ne ma yasa galibin masana ke ganin cewa, ita ce jagora a dukkan bangarorin jikin dan adam. (Nan gaba za mu gani, shin wannan tabbaci haka yake a yanzu?).

Kwakwalwa na gudanar da ayyukanta ne ta hanyar wasu sinadaran maganadisun lantarki (watau Neurons) da ke makare cikin jijiyoyin da ke cikinta (watau Nerves), wadanda ke aika sakon sadarwar bayanai zuwa sauran bangarorin jiki, ta hanyar wani tsarin sadarwa mai ban al'ajabi. Wadannan bayanan sadarwa na dauke ne cikin abubuwa guda biyu; da sinadaran jiki (Chemical) da ke dauke cikin yadin jijiya (Nerve Cells). Sai kuma ballin maganadisun lantarki (watau Electrical Pulse). Wadannan su ne madaukan bayanai da ke aiwatar da sadarwa daga kwakwalwa zuwa sauran bangarorin jiki, ta hanyar kwayoyin halittar sadarwa da ake kira Neurons, wadanda ke amfani da sinadaran maganadisun lantarkin sadarwar da ke cikinsu da ake kira Neurotransmitters. Kowane Neuron na dauke ne da rassa da ke karba ko mika bayanan da ya sarrafa zuwa wani Neuron din. Wadannan rassa dai sun hada da Dendrites, da kuma Axons, wadanda su ne kamar ressan sadarwa tsakanin kwayoyin halittar kwakwalwa, don aiwatar da sadarwa na bayanai ko sinadarai a tsakaninsu.

An gunadar da bincike masu dimbin yawa kan kwakwalwar dan adam, da irin kudurar da Allah ya nuna a cikinta, wajen iya sarrafa bayanai da sadar da su ga sauran bangarorin jikinsa. Binciken baya-bayan nan da aka gudanar mai alaka da kwakwalwa kai tsaye shi ne wanda Roger Sperry ya gudanar kan tsarin gudanarwar kwakwalwa, tsakanin bangaren hagu da bangaren dama. Ya fitar da sakamakon bincike ne da ke nuna cewa, mutane sun sha bamban wajen tunani ne saboda irin bangaren da suke tunani da shi daga kwakwalwarsu. A karshen bincikensa ya tabbatar da cewa, bangaren kwakwalwar dan adam na hagu shi ne wanda ke taimaka wa dan adam tunani ta hanyar dabi'a. Ma'ana, dukkan abin da dan adam ya ci karo da shi na bayanai ko gwagwarmayar rayuwa, yakan sarrafa bayanan ne a tsarin da Allah ya halicce shi da ita na tunani, don fitar da sakamako. Misali, idan mutum ya fito daga gidansa, ya baro iyalinsa a ciki, yana fitowa sai ya ci karo da babban amininsa da ya saba zuwa gidansa, suna gaisawa sai abokinsa yace ya zo ne su gaisa da iyalinsa, abin da wannan mutum zai ayyana kawai shi ne, gaisuwa ce ta yau da kullum. Ba wata damuwa.

Amma bangaren kwakwalwa na dama kuma shi ne ke taimakawa wajen tara bayanai, da irin yanayin da abubuwa ke faruwa, da dalilan da suka sa su faruwa, kafin fitar da hukunci kan wani abin da ya faru a lokacin Magana. A misalin da muka kawo a sama, mai tunani da bangaren damansa ba zai amince cewa gaisuwa ce kadai ta kawo wannan abokin nasa ba. Har sai ya yi la'akari da irin lokacin da abokinsa ya zo (da safe ko da rana ko da yamma ko da dare?), da irin yanayin da yazo a ciki (farin ciki ko bakin ciki?), da irin yanayin da alakarsu ta abota take ciki (suna cikin shiri ne ko bayan sun bata?), sannan zai yanke hukunci ko gaisuwar ta Allah-da-Annabi ce ko kuma da wata a kasa. A takaice dai, an gudanar da bincike da dama kan kwakwalwar dan adam, kuma ana kai. Ba don komai ba sai don irin muhimmancin da ke tattare da wannan gaba na jikinsa.

About Author  
 Picture
Ahmad Abdulnasir Shuaib
TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 1 Blog Post Header Image TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 2 Header Image TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 3 Blog Post Header Image TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 2 Header Image

Imagination is more important than knowledge. Life is like riding a bicycle. To keep your balance you must keep moving. If you can't explain it simply, you don't understand it well enough.
--- Albert Einstein

Do you want to get informed about new articles?